Features Ko kun San?
Ko kun san manhaja ce dana tsara ta domin kawo muku abubuwan daya kamata ace kun sani waÉ—an zai yi wuya ace kun same su a wani guri domin na tattaro bayanan dake cikin wannan manhajarce daka sassa daban daban.Irin wannan manhajar zata kunshi bayanai masu tarin yawa don haka na tattaro abubuwan da nake ganin cewa zasu fi É—aukan hankali ne kawai.
Domin koda na sanya bayanai miliyan É—aya ne banyi tsammanin na kammala ba.
na tattaro bayanai da suka shafi tarihi, kimiyya da fasaha, psychology da sauran fannoni.1.
Ko kun san Annobar yunwa mafi muni da aka taɓa yi a tarihin duniya ita ce wacce aka yi a shekara ta 1932 zuwa 1933 a ƙasar Sin (China) inda mutane sama da miliyan arbain suka rasa rayukansu sanadiyyar wannan balain yunwar.2.
Ko kun san Yaƙi mafi muni da aka taɓa yi a tarihin Nigeria shine yaƙin basasar shekara ta 1967, wato yaƙin biafra, lokacin da iyamurai suka ayyana ɓallewa daga Nigeria.
Kimanin mutane miliyan ɗaya suka rasa rayukansu sanadiyyar wannan yaƙin.3.
Jihar Kano itace jiha mafi yawan jamaa a Nigeria.4.
Lalacewar ƙwaƙwalwa zai iya aukuwa ne kawai idan zafin zazzaɓi ya kai 107.6° farenheit.5.
An yi dashen zuciya na farko ne a 3 Dec 1967.6.
Tururuwa basa yin barci.
7.
Baza ka iya kashe kanka ta hanyar riƙe nunfashinka ba.8.
Cakuleti zai iya kashe karnuka, domin ya ƙunshi sinadarin theobromine wanda yake shafan zuciyoyinsu da jijiyoyi.9.
Dodon koƙi zai iya yin barcin shekaru uku.10.
Zuma ce kawai abincin da baya lalacewa.
11.
Idanun jarirai ba za su iya yin hawaye ba har sai sun kai makonni shida zuwa takwas a duniya.
12.
Nigeria wacce take da yaruka 521, itace ta huÉ—u a yawan yaruka a duniya.13.
Turawan ƙasar Portugal sun iso Nigeria a shekara ta 1472.14.
A shekara ta 1880 Turawan Birtaniya suka fara mamaye kudancin Nigeria, amma sai a shekara ta 1903 suka fara mamaye arewacin Nigeria.
Domin sanin waÉ—annan bayanan dama wasu sauran É—aruruwan bayanai sai ka saukar da wannan manhajar.
Secure & Private
Your data is protected with industry-leading security protocols.
24/7 Support
Our dedicated support team is always ready to help you.
Personalization
Customize the app to match your preferences and workflow.
See the Ko kun San? in Action
Get the App Today
Available for Android 8.0 and above